1 Yuli 2016 - 15:11
Ranar Quds Ranar Kare Al'ummar Palastinu Da Ke Karkashin Zalincin Yahudawan Isra'ila

A yau ne ranar Juma'ar karshe ta watan Ramadan al'ummomi daban-daban na duniya ke gudanar da tarukan ranar Quds, domin nuna goyon baya ga al'ummar Palastinu da ke karkashin zaluncin yahudawan Isra'ila, da kuma jaddada alkawali na kare wurare masu tsarki da ke palastinu, wanda masallacin Quds ke kan gaba.

Gwamnatin kasar Iran ta sanar da cewa, za a fara gudanar da jerin gwano na ranar Quds ta duniya a garuruwa 850 na a kasar daga karfe goma da rabi na safiyar yau, inda dukkanin al'umma gami da malamai na sunna da shi'a na kasar baki daya za su fito a cikin sahu guda, domin nuna goyon baya ga al'ummar Palastinu, da kuma jaddada wajabcin 'yantar da masallacin Quds mai alfarma daga mamamyar yahudawa.

Marigayi Imam Khomeni wanda ya assasa Jamhuriyar muslunci ta Iran ne dai ya ayyana wannan rana ta Juma'ar karshen kowane watan ramadan ta zama ranar Quds ta duniya, domin raya ruhin al'ummar musulmi dangane da mamayar da yahudawan sahyuniya suke yi a kan wannan masallaci mai tsarki, alkiblar manzon Allah (SAW) ta farko, da kuma nuna goyon baya ga Palastinawa da ke karkashin zaluncin yahudawa.288